Yayin da karancin mai ke cigaba da barazana ga harkokin yau da kullum a Najeriya – musamman ma yankin arewa - masu sana’ar saye da sayar da mai a Najeriya na korafin cewa sun zuba kudadensu a depot-depot ciki har da ne NNPC amma an kasa bas u mai din, al’amarin da ya ce na daya daga cikin musabbabin rashin mai din.
Mataimakin Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur, Alhaji Abubakar Mai Gandi ya ce dama can su depot-depot masu zaman kansu na sayar da man ne sama da farashin gwamnati. Kuma duk da sun saya a hakan, an kasa bas u man. Y ace masu depot-depot din sun ce abin da ya sa su ka ki ba da man shi ne, rangwamen da gwamnati ta kan bas u don sayar da man da sauki har yanzu ba a bas u ba duk kuwa da koke-kokensu. Y ace hatta ita kanta hukumar NNPC wadda ta gwamnatin tarayya ce, ta kasa sa kamfaninta ya samar da mai din duk kuwa da cewa ‘yan kasuwan sun biya.
Alhaji Mai Gandi ya ce da farko matatun man da aka kyara sun fara aiki amma yanzu su ma sun tsaya. Ya ce dole ne gwamnati ta saka ido ta tabbatar cewa kayan gyarar da ta yi odansu sun iso kuma komai na gudana kamar yadda ta ba da umurnin a yi.
Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton: