A yau Talata, Hukumar Kula da Cinikayyar Albarkatun Man Fetur a Najeriya (NMDPRA), ta gana da manyan dillalan man fetur da nufin magance matsalar yawan samun karancin man a kasar.
Shugaban Hukumar ta NMDPRA, Farouk Ahmed, wanda ya shaidawa manema labarai yadda ganawar ta wakana, ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewar mamallaka rumbunar adana mai da mambobin Kungiyar Dillalan Man Fetur Mai Zaman Kanta (IPMAN) ba zasu dakatar da samarda man ba kasancewar NMDPRA ta fara shirye-shiryen biyan mamallaka rumbunan adana man basussukan da suke bi bayan tantance takardunsu.
A watan daya gabata, IPMAN tayi barazanar durkusar da harkar samarda man fetur a Najeriya, akan rashin biyan bashin Naira biliyan 200 ta kudaden dakon man.
Har ila yau, shugaban Hukumar ta NMDPRA ya bayyana cewar manyan dillalan man sun koka akan gazawarsu ta shigo da albarkatun man fetur cikin kasar nan.
Ya kuma baiwa dillalan man tabbacin cewar samun karin tagomashi irinsu matatar man Dangote zai kawo sauki duk da cewar a matsayinsu na ‘yan kasuwa, suke da zabin inda zasu sayo kayansu.
Ahmad ya kuma kara da cewar sun tattauna sosai akan shirin gwamnatin tarayya na komawa amfani da motoci masu amfani da iskar gas din CNG.
Don haka ya bukaci manyan dillalan man dasu duba yiyuwar samar da wuraren shan iskar gas din ta CNG a gidajen mansu kasancewar Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bada umarnin cewar wajibi ne dukkanin motocin da gwamnatin tarayya zata saya anan gaba sun kasance masu amfani da gas din CNG.