Kimanin korafe-korafe 177 da suka shafi kwangilolin da aka bayar a ofishin ministan tsaron Nijer tsakanin shekarar 2017 zuwa 2019 ne ke kan teburin alkali mai tuhuma Procureur de la repunlique, a matsayin kamalallen rahoton binciken da gwamnatin Nijer ta ce ta gudanar game da inda aka shiga da wasu dubban miliyoyin CFA da suka yi batan dabo.
Nouhou Mahamadou Arzika, na daga cikin jagororin kungiyoyin da suka matsa wa gwamnati lamba don ganin an yi haske a wannan badakala. Ya ce duk wanda yayi ba daidai ba, to ya kamata a hukunta shi yadda ya kamata ba sani ba sabo.
A ra’ayin Abdourahamane Alkassoum, wani mai sharhi akan al’amuran yau da kullum, damka wannan harka a hannun mashara’anta ita ce hanya mafi a’ala wajen ba kowanne bangare hakkinsa a dokace.
To sai dai shugaban kungiyar MPCR, mamba kuma a hadakar kungiyar CCAC Nouhou Arzika, ya ce dole ne a binciki abubuwan da suka faru a ma’aikatar ta tsaro tun daga shekarar da shugaba Issouhou Muhammadou ya dare karagar mulki kawo yau. A yanzu dai kallo ya koma wajen alkalan shari’a.
Badakalar kudaden makamai a ofishin ministan tsaro wani abu ne da aka jima ana takun saka akansa tsakanin gwamnatin Nijer da shugabannin kungiyoyin fararen hular da suka nace akan bukatar ganin an hukunta wadanda suka wawure wadanan dubban miliyoyi, lamarin da ya yi sanadiyar garkame wasu ‘yan fafutika a gidajen yarin yankin Tilabery yau makwanni sama da 3.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5