Nijar: 'Yan Ta'adda Sun Umurci Jama'ar Chinagoder Su Fita a Garin

Mazauna garin Chinagoder da 'yan bindiga suka kashe dakarun Nijar da dama a 'yan kwanakin nan, sun tsere zuwa garuruwa makwabta.

Al'umar garin ta fice ne bayan da ‘yan ta’adda suka ba ta wa’adin ficewa ko kuma su fuskanci fushinsu.

Lamarin na zuwa ne mako guda bayan harin da ya halaka dumbin sojoji a barikin na Chinagoder da ke kan iyakar Nijar da Mali.

Bayanai daga kauyen Chinagoder na cewa, daukacin mazauna garin sun yi hijira zuwa garuruwa daban-daban na yankin Tilabery don gujewa ‘yan bindigar.

Umurnin na zuwa ne duk kuwa da cewa yankin na karkashin ikon hukumomin Jamhuriyar ta Nijar.

Malan Abdou Mahaman, daya daga cikin magidanta da suka tsere zuwa garin Abala, ya ce ‘yan bindigar da suka kai hari ne suka kore su daga Chinagoder.

A cewar shi, yanzu garin ya watse, kuma wasu sun nufi Banibangou, wasu sun gudu zuwa garuruwa makwabta, ga mata ga yara kanana, sun bar dukiyoyinsu.

Ya kara da cewa, a halin yanzu, ba su da abinci ba muhalli, dalilin da ya sa suke kira da a taimaka masu.

Tuni dai mahukunta a garin Abala tare da hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu suka fara nazarin hanyoyin tunkarar wannan sabon al’amari.

Jami’in fafutuka a yankin, Maman Haldi, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, suna daukan matakan da suka dace.

A halin da ake cikin dai, ba'a samu jin tabakin Gwamnan jihar Tilabery ba.

Da ma dai masana sun bayyana cewa, ‘yan ta’addan kasar Mali na amfani da hanyoyin sadarwa irin na zamani domin cusa rudani a kawunan jama’a musamman a karkara, abin da ake ganin shi ne ya fara tasiri a Chinagoder.

Ga cikakken rahoto cikin sauti daga Nijar.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: 'Yan Ta'adda Sun Umurci Jama'ar Chinagoder Su Fita a Garin