Ofishin jakadancin Amurka da ke Jamhuriyar Nijar, ya ba da kyaututtuka ga wasu 'yan jarida shida da suka yi fice a gasar rubuce-rubuce da ta shirya.
Wasu daga cikin 'yan jarida, su kimanin shida wadanda suka lashe gasar, sun hada rahoto kan matsalar matasa da ta'addanci, illar rubuce-rubuce a yanar gizo a wani bangaren, da zamantakewa tsakanin addinai mabanbanta, da muhimmancin noma tushen arziki, da dai sauran su.
An ba da tukwici na million daya ga 'yan jarida uku, sauran ukun aka ba su jaka 400, hakan ne ya sa tawagar da ke kunshe da kungiyoyin matasa, da na mata 'yan jarida, su ma suka ba da gudumuwarsu, don kawo karshen irin kalubalen da ke damun 'yan jarida.
An horar da 'yan jaridar ne kan yadda za su gudanar da aikinsu cikin tsanaki, da bin doka da yadda za su gamsar da al'umma, wanda kasar ta Amurka ta dauki nauyi.
Ga cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.
Your browser doesn’t support HTML5