Nijar: 'Yan Fafutuka Zasu Samu Tallafin 200 Miliyan cfa

A wani yunkurin karawa kungiyoyin kare hakkin dan Adam kwarin gwiwa a Jamhuriyar Nijar, Tarayyar Turai da hadin gwiwar hukumar kare hakkin dan Adam ta CNDH sun kaddamar da wani shirin da zai mai da hankali wajen tallafawa kungiyoyin.

Kimanin miliyan 200 na cfa ne kungiyar tarayyar turai ta kudiri aniyar kashewa kungiyoyin kare hakkin dan adam a tsawon shekaru 2 a karkashin wani shirin da aka yiwa lakabi da Projet Appui aux defenseurs des droits Humains da nufin karfafa jami’an fafitika.

Wannan ya faru ne bayan la’akari da irin kalubalen da suke fuskanta kamar yadda wakilin kungiyar EU a Nijar Olai Voionmaa ya bayyana a yayin bukin kaddamar da aiyukan wannan shiri.

Ya ce sau da yawa zaka ga masu kare hakkin dan adam suna ta fama gwagwarmaya su kadai ko a kungiyance kuma duk da matsin lamba ko barazanar da suke fuskanta, ba abinda ke katse masu hanzari saboda haka kungiyar tarayyar turai a shirye take ta basu kariya kuma ta kare mutuncinsu.

Shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula na Reseau Esperence Maman Bachar ya jinjinawa wannan yunkuri na kungiyar EU domin a cewarsa mataki ne da zai kare ‘yan gwagwarmaya daga kwadayin abin duniya.

Mayar da son rai shara, kafin a kasafta wadanan kudaden tallafi ya zama wajibi kafin tantance kungiyoyin da suka cancanci cin moriyar wannan tsari domin ta haka ne za a iya cimma burin da aka sa gaba.

Jamhuriyar Nijar ta yi kaurin suna a wajen kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasa da kasa a ‘yan shekarun nan sakamakon lura da yadda hukumomin kasar suka sha hanawa masu fafitika ‘yancin gudanar da zanga zanga matakin da gwamnatin ta Nijar ke alakantawa da dalilan tsaro.

A saurari rahoto cikin sauti daga birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: 'Yan Fafutuka Zasu Samu Tallafin 200 Miliyan cfa