A jamhuriyar Nijar 'yan adawa sun gudanar da taron gangamin a yau Lahadi a birnin Yamai da nufin nuna rashin jin dadinsu akan yadda hukumomi ke rikon sakainar kashi ma sha'anin tsaro a yankunan da ke fama da hare haren ta'addanci, duk kuwa da cewa gwamnatin na ikirarin kashe wa fannin tsaro makudan kudade a 'yan shekarun nan.
Dubban magoya bayan jam’iyun kawancen adawa na Front patriotique et republicain ne suka hallara a taron gangamin da ya gudana a dandalin place de la concertation dake kofar majalisar dokokin kasa.
Yanayin tabarbarewar tsaron da ake ciki a jihohin Tillabéry da Tahoua da Diffa na daga cikin matsalolin da ke damun jam’iyun hamayya na Front Patriotique a yau, kamar yadda jagoransu Kanar Ibrahima Yakuba (murabus) ya bayyana.
Wannan gangami da ke gudana a wani lokacin da Shugaba Issuhu Mahammadu ke ci ka shekaru 8 da darewa akan karagar mulkin Nijar, ya kasance wata damar yin waiwaye akan alkawuran da shugaban ya dauka a watan Afirilun 2011, kamar yadda kakakin gamayyar jam’iyyun (FRDDR), Mamman Sani Adamu ya jaddada.
A ci gaban jawabinsa a yayin wannan gangami, tsohon Ministan harakokin wajen Nijar a gwmnatin falkawa ta 1, Ibrahima Yakuba ya bukaci ‘yan kasa su dage da gwagwarmaya don lashe zabubukan 2021.
Da yake bitar ayyukan da ya gudanar a tsawon shekaru 8 na mulkinsa, Shugaba Issuhu Mahammadu ya bayyana gamsuwa da abinda ya kira kyawawan sakamakon da gwamnatinsa ta samu, wanda ya tahallaka kan ayyukan ci gaban kasa, duk kuwa da irin kalubalen tsaro da na canjin yanayi da na faduwar darajar ma’adanai da ake fuskanta, yana mai alfahari da kashe wa fannin tsaro kashi 15 daga cikin 100 na tsarin kasafin kowace shekara.
Ga wakilinmu Sule Barma da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5