Nijar Ta Sake Asarar Jami’an Tsaro

Lokacin jana'izar dakarun Nijar da suka rasa rayukansu a harin Inates kafin wannan hari na Tillabery

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da rasuwar jami’an tsaron kasar kimanin 14 sakamakon wani harin ta’addancin da aka kai a karkarar Sanam da ke gundumar Abala A yankin Tillabery.

Harin ya faru ne a daidai lokacin da wani ayarin jami’an tsaron ke yi wa jami’an hukumar zabe rakiya akan hanyarsu ta zuwa aikin rajista.

Sanarwar da gwamnati fitar, ta kara da cewa askarawan na Nijar sun karkashe ‘yan ta’adda da dama a yayin wannan fada.

Amma babu bayanai da suka nuna yawan 'yan ta'addan suka mutu.

Lamarin ya wakana ne da misalin karfe 3 a ranar Laraba.

Sanarwar wacce ta hadin gwiwa ce ta kara da cewa, jandarmomi 7 da "Garde Nationale" 7 ne suka kwanta dama a sakamakon wannan hari.

Har ila yau ana neman wani jami’in tsaro daya da ya yi batan-dabo.

Ana su bangare, askarawan gwamnatin ta Nijar sun yi nasarar halaka dumbin maharan, ko da yake, ba a bayyana adadinsu ba.

Tuni dai ‘yan kasa suka fara nuna damuwa kan wannan al’amari mai matukar daure kai.

Harin na karkarar Sanam na faruwa ne a wani lokacin da ‘yan Nijar ke ci gaba da nuna juyayi kan rasuwar sojojin nan 71 na barikin Inates da aka kashe.

Hakan na kuma kara nuna bukatar karfafawa jami’an tsaro kwarin gwiwa a wannan yaki da ya addabi kasashen yankin Sahel.

A halin da ake ciki, Kungiyoyin fafutuka na CCAC ta kuduri aniyar shirya jerin gwano da gangami a ranar Lahdin da ke tafe.

Za a gudanar da gangamin ne a daukacin biranen kasar da nufn nuna goyon baya ga dakarun tsaro.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Ta Sake Asarar Jami’an Tsaro - 2'24"