Sama da mutane 1,500 da ke sana’ar safarar bakin haure suka ci moriyar wani tallafin taimaka masu canza sana’a, ganin cewa hukumomin Nijar sun haramta duk wata harka da ke da nasaba da sana’ar bakin haure.
Wadannan adadi na cikin mutane 6,565 da ke yin sana’ar a can baya a jihar Agadez.
Muhammedo Anako shi ne shugaban majalisar jihar Agadez kuma ya kasance a wurin bikin tallafawa mutanen.
Ya ce tallafin, an mika shi ga wata kungiya mai zaman kanta da ake cewa ONG Karkara. Tallafin ya shafi yankuna guda shida na jihar kuma zai lakume kudin Euro miliyan 3.5.
Malama Manema Muhammad shugabar kungiyar da ke kokarin kawowa masu safarar mutane tallafi a jihar Agadez ta tabbatar cewa cikin wadanda suka samu tallafin akwai mata 679 da za su samu Sefa miliyan 981.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5