Gwamnatin Jamhuriyar Nijer da hadin guiwar Amurka da majalisar dinkin duniya sun shirya wani taron horo na musamman domin jami’an tsaron kasar, da nufin karantar da su mahimman dubarun tattara hujjojin da ke da nasaba da ayyukan ta’addanci.
Jakadan Amurka a Jamhuriyar Nijer Eric P. whitaker a yayin bikin bude taron, ya ce “kowa ya taka doka to doka ta taka shi”.
Jami’in hulda da ‘yan jarida a ofishin jakadancin Amurka Alhaji Idi Barau, ya yi bayani akan makasudun yunkuri na hadin guiwa. In da ya ce, bin tsarin doka wajen gurfanar da wanda ake zargin ya aika ta laifi, shine abin da ya dace.
Kungiyoyin kasa da kasa sun jinjinawa yunkurin na Jamhuriyar Nijer, sakamakon lura da yadda kasar ta kafa wata kotun musamman mai alhakin hukunta mutanen da ake zargi da ta’addanci.
Mukaddashin ministan shari’a, Maman Waziri na ganin wannan horo zai taimaka a kaucewa tangardar da aka fuskanta a can baya.
Taron horon ya baiwa bangarori damar saka hannu akan wata yarjejeniyar gudanar da aiki kafada da kafada, tsakanin ofishin ministan tsaron Nijer, da na ministan cikin gida da takwaransu na shari’a.
Amurka da majalisar dinkin duniya reshen yaki da fataucin miyagun kwayoyi da aikata miyagun laifika, wato ONU DC ko UNODC, ta ce matakin wakiliyar hukumar Elena Rigacco Hay, ya yi dai dai da shawarwari da aka yi a yayin wani taron da aka gudanar a baya bayan nan a Abuja kan batun tattara hujjojin fayyace ayyukan ta’addanci.
Rashin hukunci na daga cikin abubuwan da jama’a ke korafi akansu a kasashen sahel masu fama da ta’addanci, yayinda gwamnatoci da kungiyoyin kare hakkin dan adam ke jan hankalin gwamnatoci sun bi hanyar mutunta dokokin kasa da kasa.
Ga rohoton Wakilin muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma, cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5