Duk da cewa hukumomi da kungiyoyin kare hakkin dan adam sun shafe tsawon shekaru suna fafutukar kawar da sha'anin bautar da dan adam a Jamhuriyar Nijar, har yanzua al'amarin na ci gaba da wanzuwa a wasu yankunan kasar.
La’akari da yadda dabi’ar bauta ke kara tsananta ya sa kungiyoyin yaki da bauta a kasashen yammacin Afrika hada karfi domin tunkarar wannan kalubale.
A kan hakan ne su ka gudanar da taron shekara-shekara a Yamai don zakulo hanyoyin da za'a bullowa wannan lamari kamar yadda
Sakataren kungiyar Timidria Ali Bouzou ya yi wa Muryar Amurka karin bayanin cewa "hakika akwai matsalar bauta har yanzu a Nijar da ma wasu makwabtan kasashe kamar Mali da Maurtaniya, don haka ya kamata gwamnati ta kebe rana ta musamman domin tattauna wannan matsala".
A cewar darektan ofishin ministan shari’a Chaibou Maman, gwamnatin Nijar na adawa da wannan dabi’a ta bauta saboda haka za ta hada gwiwa da kungiyoyin kare hakkin dan adam a wannan yaki.
Ya ce "tun a wani zaman da firaiminista Birgi Rafini ya jagoranta a bara gwamnati ta amince da bukatar ware ranar yaki da bauta ta kasa kuma ina jaddada ma ku cewa shugaban kasa da fraiminista suna Allah wadai da wannan dabi’a ta bauta saboda haka ne ma gwamnati ta kafa dokoki da ma’aikatu domin tunkarar wannan al’amari."
Kundin tsarin mulkin jamhuriyar Nijar ya bayyana cewa dukkan ‘yan kasa matsayinsu daya a gaban doka haka kuma ya kara nanata cewa Nijar da al’umarta sun yi na’am da yarjejeniyar kasa da kasa akan maganar hakkin dan adam ta ranar 10 ga watan December 1948.
A saurari cikakken rahoton Suley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5