Sunki dari tara da sha bakwai na tabar wiwi, kwatankwacin kg dari takwas da sha biyu ne aka kama a hannun wasu ‘yan Nijar uku dukkansu matasan da shekarunsu ba su wuce talatin ba. Dubun wadannan masu safara ta cika ne a sakamakon wasu bayanai da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi (OCRITIS) ta tattara a garin Gaya da ke iyakar Nijar, Najeriya da jamhuriyar Benin.
A wani abinda ke zaman sabon salo, masu wannan haramtacciyar sana’a sun fara bi ta ruwa da nufin kauce wa tashoshin bincike, kamar yadda daraktan ofishin kula da hulda da jama’a kuma kakakin hukumar ‘yan sanda Dr Abou Mountari ya bayyana a lokacin gabatar da abubuwan da aka kama.
Hukumar ‘yan sandan ta ce gudummowar al’umma na da matukar tasiri a yunkurin murkushe safarar miyagun kwayoyi a kasar, inda a yanzu haka a ke fama da illolin wannan masifa.
Alkali mai shigar da kara a kotun Yamai Chaibou Moussa, ya ziyarci ofishin hukumar OCRITIS domin jaddada goyon bayan hukumomi a wannan kokari.
Mai shari’a Zakari Yaou Mahamadou na daga cikin mukarraban hukumomin shari’a, ya ce ofishin na bakin aiki tukuru domin kama duk masu aikata wadannan laifuka kuma za a gurfanar da su a kotu.
Wannan dai shi ne karo na biyu da a kasa da mako guda dubun masu fataucin miyagun kwayoyi ke cika a Nijar, don ko a ranar Juma’ar da ta gabata ma hukumar OCRITIS ta gabatar da wasu mutane tara da ta kama dauke da dubban kwayoyi da suka fito da su daga Najeriya zuwa Libya da niyar ratsa wa ta biranen Maradi da Agadez, haka kuma a wannan rana an gabatar da wani dan jihar Anambra a Najeriya da ya hadiye kg 1.1 na hodar heroine a cikinsa da zummar shiga Aljeriya.
Saurari cikakken rahoton Souley Mumuni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5