Daruruwan ‘yan ta’adda ne dauke da manyan bindigogi da motoci masu silke da wadanda ke dauke da boma bomai suka kutsa barikin sojan Inates dake gundumar Ayorou a yankin Tilabery kan iyakar Nijer da Mali inda aka shafe awoyi a kalla 3 ana ba ta kashi daga karfe 3 na rana zuwa 6 na yammacin talatar da ta gabata kafin isar wani daukin da aka aika.
A wata sanarwar da darektan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro Col. Boubacar Hassane ya karanta a gidan television mallakar gwamnatin Nijer, an bayyana cewa sojojin Nijer 71 ne suka hallaka wasu 12 suka ji rauni yayinda wasu wadanda ba a bayyana adadinsu ba suka yi batan dabo. Sanarwar ta kara da cewa, an karkashe ‘yan ta’adda masu tarin yawa sai dai ba a fadi yawansu ba.
Nan da nan aka bi sawun maharan da aka ce sun nufi iyakar wata kasar da ba a ambaci sunanta ba.
Mumunar barnar da harin ya haddasa ta sa Shugaba Issouhou Mahamadou katse taron da yake halartar a kasar Masar inda shubanin kasashen Afrika ke tantauna batutuwan da suka shafi sha’annin tsaro da ci gaban wannan nahiya.
Wannan shine karo na biyu da ‘yan ta’adda ke kai hari a barikin sojan Inates domin ko a watan yulin da ya gabata ma sun yi nasarar kashe sojojin 18 to sai dai wanda aka kai a shekaranjiya talata shine hari mafi muni da aka taba fuskanta a jamhuriyar Nijer tun bayan da ‘yan ta’adda suka kaddamar da hare hare akan wannan kasa a shekarar 2015.
Harin na Inaes na zuwa ne a wani lokacin da al’umomin yankin sahel ke matsin lamba ga kasar Faransa da neman ta kwashe sojojin da ta girke a wannan yanki da sunan yaki da ta’addanci a karkashin rundunar Barkhane wace suke zargi da rashin wani hobbasa a yakin da wadanan kasashe ke yaki da ‘yan ta’adda.
Kawo yanzu ba wata kungiyar da ta dauki alhakin wannan hari dake matsayin na biyu da ake fuskanta a cikin kwanaki 2 kacal akan iyakar Nijer da Mali.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma
Your browser doesn’t support HTML5