A Jamhuriyar Nijar wasu ‘yan kasar sun fara shawartar hukumomi da su dauki matakin tallafawa jama’a da iskar gas.
Kiran a cewar kungiyoyin, na neman sassauci ne kan wahalhalun da magidanta ke fuskanta a wannan lokacin da ake fama da zaman gida domin takaita yaduwar cutar coronavirus.
A kwanakin baya, hukumomin sun daukewa masu karamin karfi kudaden wutar lantarki da ruwan sha a matsayin wani bangare na matakan sassauta wahalhalun talakawa a wannan lokaci na annobar COVID-19.
Sannu a hankali, kiraye-kirayen jama’a na karuwa a kafafen sada zumunta da nufin ganar da gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar bukatar ta tallafawa ‘yan kasar da iskar gas.
Amfani da gas a kasar ya zama jiki ga al’umar birane da karkara saboda yadda aka fara fahimtar illolin sare itace.
Wani dan farar hula, Ingay Issouhou, na daga cikin masu kokarin ankarar da hukumomi tasirin ba da irin wannan tallafi a wannan lokaci na annoba.
“Yadda muka mallaki ruwanmu, haka muka mallake iskar gas dinmu. A ba mu kawai mu ci bulus saboda mutane su samu sauki,” a cewar Issouhou.
Iskar gas na daga cikin albarkatun da ake samarwa a Nijar tun bayan da kasar ta fara hako man fetur dinta tare da tace shi anan cikin gida yau kimanin shekaru kusan 9.
Hakan ya sa kungiyoyin ci gaban jama’a ke ganin ya zama wajibi a bai wa ‘yan kasa damar morar wannan arziki.
Your browser doesn’t support HTML5