NIJAR: Kungiyar Matasa Musulmi Ta Yi Taron Bude Baki Da Kiristoci

Taron limaman masallatai, matasa musulmi da kiristoci wajen bude baki a Konni

A Jamhuriyar Nijar wata kungiyar matasan Muslmi ce ta shirya taron bude baki a Birnin Konni inda ta gayyato limaman masallatan Juma’a da kungiyar kiristoci su sha ruwa tare

Wata kungiyar matasa Musulmi ta Birnin Konni ta shirya taron bude baki da limaman masallatan Juma’a da kungiyar kiristoci domin tabbatar da zaman lafiya.

Malam Munkaila Sarka shugaban wurin bude bakin y ace sun bincika babu matsala tsakanin musulmi da kirista dalili ke nan da suka shirya taron domin kowa ya fahimta cewa mabiya addinan biyu na zaman lafiya da juna.

Shi ma mataimakin shugaban kungiyar matasan Usman Ubandoma ya yaba da haduwar musulmi da kirista domin yin bude baki albarkacin watan azumi.

A nasa bangaren shugaban kungiyar kiristoci Fasto Abubakar Musa ya yaba da taron saboda yana tabbatar da kwanciyar hankali da kuma rahama da daukakar Allah a cikin kasarsu ta Nijar. Taron zai tabbatar da zumunci inda za’a ba juna daraja.

Mai Martaba Sarkin Konni Alhaji Ibrahim Salihu ya nuna murnarsa game da husahar matasan da suka shirya taron tsakanin musulmi da kiristoci. Y ace a zamantakewa yana da kyau mutane su yi la’akari da abubuwan dake kawo masu ci gaba kullum ba wadanda suke maidasu baya ba. Taron da matasan suka shirya wani zarafi ne na rokon Allah ya tabbatar da zaman lafiya a kasar Nijar ta kuma ci gaban ta.

A saurari rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

NIJAR: Kungiyar Matasa Musulmi Ta Yi Taron Bude Baki Da Kiristoci – 3’ 41”