A jamhuriyar Nijar, wata kotu ta sallami wani jami’in fafutuka Abbas abdul’aziz, da mukarrabansa biyu wadanda aka kama bayan tarzomar da ta barke a Yamai ranar 29 ga watan Oktoba, lokacin da suke gudanar da wani gangamin nuna kiyayya da tsarin kasasfin kudin shekarar 2018.
An kama Adbudul’aziz bayan zargin sa da aka yi na gudanar da taron da ya rikide zuwa zanga zanga har aka yi kone kone da fashe fashe yayin da wasu matasa suka yi kokarin shiga farfajiyar majalisar kasa a Yamai. Hakan ya janyo offishin ministan cikin gida ya bukaci a rufe kungiyar kafin a kama shuwagabanin ta.
Bayan zaman wakafi na makonni sama da 3 alkalin kotun Yamai, ya sallami Abbas Abdul’aziz, tare da mukarabansa bisa la’akari da cewa ba kamshin gaskiya akan abubuwan da ake zargin su da aikatawa.
Abbas Abdul’azizi ya bayyana wa wakilin Muryar Amurka, cewa yana da gaskiya kuma bai aikata laifin da ake zargin sa dashi ba.
Wakilin Muryar Amurka a Yamai, Sule Mumini Barma ya aiko mana da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5