Yayin da kungiyar IS ta ke rasa mafi yawan yankunan da ke hannunta da kuma karfin ikonta a Syria da Iraqi, gwamnatocin kasashen yankin Arewacin Afirka, sun ce suna fargabar dawowar mayaka daga fagen yaki a Gabas ta Tsakiya, Ka iya haifar da rikici a yankunansu.
“Yankin na fuskantar barazana… idan mayakan suka dawo,” inji Ministan harkokin wajen Algeria, Abdul Qader Messahel, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Birnin Alqahira.
A ‘yan kwanakin nan, rahotannin sun yi nuni da cewa, akalla mayakan kasashen waje 5,600 ne suka baro fagen yaki bayan da aka samu galaba akan IS a Syria da Iraqi.
Daruruwan mayaka daga kasashen Arewacin Afirka, da suka hada da Tunisia da Morocco, sun riga sun koma kasashensu, a cewar wani rahoto da Cibiyar Soufan ta fitar, wacce ke da hedkwata a Birnin New York, take kuma bibiyan al’amuran da ke faruwa a yankin.
Facebook Forum