Nijar: Jami’an Hukumar Kwastam Sun Shiga Yajin Aikin Kwanaki Biyu

Bikin Bude Ma'aikatar Shige da Fice a Nijer

Jami’an hukumar kula da shige da fice Kwastam na jamhuriyar Nijar sun fara yajin aikin kwanaki biyu da nufin nuna rashin nuna rashin jin dadinsu game da tsarin daukar sabbin ma’aikata na gwamnatin kasar.

Kungiyar jami’an Kwastam ta SNAD ce ta kira wannan jajin aikin kan zargin an takfa satar ansa a jarabawar neman aikin Kwastam ta baya baya nan, duk da cewa kotun raba gardama ta Conseil d’Etat ta tabbartar da halarcin jarabawar.

Tun shekarar 2018 ne hukumomi suka shirya wata jarabawa da nufin samar da kwarin kwararrun ma’aikata a hukumar Kwastam, sai dai fitar da sakamakon jarabawar ke da wuya ma’aikatar Kudi ta soke jarabawar saboda zargin anyi badakala yayin gudanar da jarabawar.

Hakan ya sa wadanda suka sami nasarar jarabawar suka shigar da kara kotun Conseil d’Etat, wadda ita kuma ta basu damar fara aiki. Sai dai lamarin ya ci tura har ta kai ga ma’aikatan sake shigar da kara a karo na biyu don sanar da kotu halin da ake ciki.

Bayan kwashe ‘yan makwanni ministan kudin kasa, Dr Ahmed Djidoud, ya fitar da wata sanarwa dake baiwa sabbin ma’aikatan damar fara aiki a hukumar Kwastam. Lamarin da ya sa kungiyar SNAD hawa kujerar naki ga amincewa da umarnin, ta kuma kira yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.

A jajibirin wannan yajin aiki matasan da suka ci jarabawar da ake dambarwa a kanta sun shigar da kara a babbar kotun Yamai, a bisa zargin kungiyar SNAD da laifin fatali da hukuncin kotu.

Kawo yanzu gwamnatin Nijer ba ta bayyana matsayarta ba game da yajin aikin na ma’aikatan Kwastam, to amma masu fafutukar kare hakkin jama’a na gargagin kungiyar SNAD ta sauya salon gwagwarmaya.

A wata sanarwa da kungiyar SNAD ta fitar a ranar Talata ta sanar da masu shigar da kaya da masu fitar da su cewa, akwai yiwuwar fuskantar tsaiko a daukacin ofisoshin shiga da fice a fadin kasar, sanadiyar jajin aikin na ranar Laraba da Alhamis.

Domin Karin bayani ga rahotan Sule Muminu Barma cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Jami’an Hukumar Kwastam Sun Shiga Yajin Aikin Kwanaki Biyu - 3'06"