Taron shuwagabanin rassa da na uwar jam’iya da ya gudana a karshen mako a Yamai ne ya yanke shawarar korar jiga jigan CDS RAHAMA cikinsu har da tsohon shugabanta Abdou Labo saboda zarginsu da kokarin haddasa rudani a tsakanin ‘yayan jam’iyar tun bayan da kotu ta bayyanashi a matsayin wanda doka ta haramtawa jagorancin harkokin jama’a.
Haka kuma shuwagabanin CDS Rahama sun bada sanarwar mayarda Moutari Kadri akan mukaminsa na mataimakin shugaban reshen Zinder yayinda suka damka ragamar shugabancin jam’iya a hannun Me Madougou Boubakar.
Da yake maida martani Dr Ibrahim Halilou wanda a kawanakin baya bangaren Abdou Labo ya nada a matsayin shugaban CDS Rahama na wucin gadi ya yi watsi da wannan mataki na korarsu daga jam’iya.
Jam’iyar wace a karkashinta Mahaman Usman ya shugabanci kasar Nijar a zamanin jamhuriya ta uku, ta yi fama da rikicin shugabanci inda aka shafe shekaru kusan hudu ana tafka shara’a tsakanin bangaren Abdou Labo da na Mahamman Usman kafin a karshe a bayyana Labo a matsayin wanda yafi cancantar ya jagoranci jam’iyar.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma
Your browser doesn’t support HTML5