Malam Abdurahamane magatakardan majalisar koli ta addinin islama ta Nijer a lokacin da yake bayyana ganin watan a kafofin yada labarai na kasar yace “yan uwa a addinin islama, a yau talata 11 ga watan mayu 2021, majalisar koli ta addinin islama ta Nijer, tana farin cikin sanarda ku cewa, an ga jinjirin watan Shawwal a cikin garuruwa da dama na wannan kasar wanda ke nuna mun kamalla azumin ramadan na 1442.”
Fara-ministan jamhuriyar Nijer malam Uhumudu Mahamadu yayi anfani da wannan damar domin taya musulmin Nijer murna kamalla azumin ramadan na wannan shekara.
Sai dai wannan sallar karshen azumin na zuwa ne a daidai lokacin da yan ta'adda ke kara zafafa hare - haren su a wannan kasar ta mu tare da hallaka fararen hulla da dakarun wannan kasar.
Karin bayani akan: islama, Ramadan, Nijer, Birnin Yamai, Nigeria, da Najeriya.
Shima Lampo shugaban kiristoci na cocin babban Birnin Yamai cewa yayi “muna muku fatan alheri albarkacin karshen wannan watan azumi da kuka yi kuma mun san irin wahalhallun da kuka yi fama da su daga tsananin zafin rana da tsadar rayuwa da ma hare - haren yan ta'adda da ke haddasa rasuwar jama'a da dama”
A yau dai a ko'ina a fadin kasar, jama'a za su fita zuwa sallar idil Fitiri tare da hukumomin kasar, inda shugaban kasar Nijer Bazum Mohamed zai halarci sallar idin a babban Birnin Yamai.
Saurari cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5