Nijar: Gwamnati Ta Kafa Dokar Ta Baci A Yankin Tiilabery

Nijar

A ci gaba da daukar matakan dakile hanyoyin da ‘yan ta’addan Arewacin Mali ke amfani da su, don kai farmaki a yankin Tiilabery, gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bada sanarwar kafa dokar Ta-Baci a gundumar Filingue.

Sai dai tuni masu rajin kare hakkin jama’a suka fara jan hankalin hukumomi akan bukatar daukar matakan samar da aikin yi ga matasa, don kare su daga tarkon ‘yan ta’adda.

A taron majalisar ministoci na karshen mako aka fidda sanarwar kafa Dokar Ta-Bacin, a gundumar Filingue a matsayin wani matakin datse hanyar da ‘yan ta’adda ke amfani da ita, wajen kaiwa-da-kawowa tsakanin kasashen Mali da Najeriya.

Sai dai hukumomi na kwatanta wannan matakin a matsayin na wucin gadi, abin da ke iya ba talakawa damar gudanar da wasu ayyukan ko sana’o'i kafin al’amura su dai-daitu.

Yi wa doka biyayya a wannan lokaci da jami’an tsaro ke kokarin murkushe duk wata barazana, wani abu ne da ya zama wajibi a wuyan talakawa. To amma mutunta ‘yancin dan adam shi ma wani batu ne da ke bukatar a duba shi, inji Mariko Aboubacar.

A nan gaba kadan majalisar dokokin kasar, za ta nazarci wannan mataki domin tabbatar da shi a hukunce, kafin nan dokar za ta soma aiki sakamakon lura da girman matsalar ta tsaro, dake kokarin mamaye baki dayan yankin Tilabery.

Saurari rahoto cikin sauti daga birnin Yamai.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Gwamnati Ta Kafa Dokar Ta Baci A Yankin Tiilabery