Nijar: Farashin Man Fetur Ya Haura Sanadiyyar Rufe Kan Iyakokin Najeriya

A cigaba da kokawa da ake yi a Najeriya da kasashe makwabta saboda rufe kan iyaka da Najeriya ta yi, 'yan Janhuriyar Nijar sun shiga kokawa da tsadar mai, wanda shi ma na da alaka da rufe kan iyakar.

Sakamakon dokar da shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Bahari ya kafa, ta hana fitowa da man Fetur ya haifar da damuwa a cikin al'umma, sanadiyyar haurawa da farashin man fetur ya yi a wajen masu saida shi a bayan fage

A cewar wasu masu amfani da man fetur, ba karamin tashin hankali hakan ya saka su ba, kasancewar dama ga matsalar da al'umma suke ciki domin tsadar kayayyakin masarufi dalilin rufe boda. Yanzu kuma ga shi an kara kudin man fetur daga dala 60 na Sefa zuwa dala 100.

Su ma dai masu saida man, acewar wani Abdulkarim, ba su ji dadin hakan ba, amma ba yadda za su yi domin ita ce hanyar neman abincinsu.

Kungiyoyin fararen hula, a ta bakin wani mambansu Malam Hararu Hamidu, na cewa ya kamata a tausaya ma talakawa, ta hanyar sassauta masu rayuwa.

Ga cikakken rahoton a sauti daga wakiliyar Muryar Amurka, Tamar Abari.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Farashin Man Fetur Ya Haura Sanadiyar Rufe Iyakokin Najeriya