Mako guda bayan da mataimakin kwamandan rundunar mayakan jamhuriyar Nijer ya zagaya yankin Diffa da nufin tayar da askarawansa daga barci, NIJARkungiyoyin fafitika na hadakar CCAC sun bayyana damuwa a game da yadda al’amuran tsaro ke kara tabarbarewa a wannan yanki inda jama’a ke tserewa matsugunansu sanadiyar yawaitar hare haren kungiyar Boko Haram da satar mutane don neman kudin fansa.
Bayanai daga yankin na Diffa na nunin gwamman fararen hula ne suka rasa rayukansu a sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram a wani lokacin da ake zaton kura ta lafa yayinda satar mutane ta zama ruwan dare a wannan yanki dake karkashin dokar ta baci lamarin da ya haddasa fargaba a zukatan jama’ar da tuni suka fara ficewa daga mahallansu. Dalili kenan da kungiyar AEC a wata sanarwa da ta fitar ta ja hankulan mahukunta.
A tsakiyar watan da muke ciki mataimakin kwamandan rundunar mayakan Nijer Janar Issa Boulama dake zagayen askarawan kasar a yankin Diffa ya umucesu da su kara jan damara a yakin da suke gwabzawa da mayakan kungiyar Boko Haram to sai dai kungyoyin fafitika na ganin wajibi ne gwamnati ana bangare ta yi aiki da wasu sharwarwarin na daban…
A karshen wannan sanarwa kungiyar AEC ta kawayenta sun nuna juyayi akan kashe kashen da suka rutsa da wasu fulanin kasar Mali a karshen makon jiya. Suna masu kiran jama’a a guji tsokano fitina komin kankantarta kasancewa duk lokacin da aka shiga fitina ba a san karshensa ba.
Your browser doesn’t support HTML5