A yankunan Diffa da Agades tururin rana nada karfin gaske to sai dai kasar Nijar bata moran wannan abun da Allah ya bata wanda kuma arziki ne.
Kwararru sun ce yin anfani da karfi da hasken rana wurin samar ma kasar makamashi ita ce hanya mafi sauki da alfanu. Kasar zata samu wutar lantarki a saukake idan tayi anfani da zafi da hasken rana domin ta samu ta kawar da matsalar wutar lantarki da yanzu ta ke fama dashi.
Shugaban kungiyar kodaye mai fafutikar kare hakkin jama'a a fannin makamashi, Alhaji Mustapha Kadi Ummani, yace masu ilimi gaba daya na duniya sun amince da cewa idan kasar tana son ta rage zafin rana to sai an bar yin anfani da wutar lantarki ta inji. Zafin rana ba sayensa ake yi ba. Allah ne ya ba dashi. Yin anfani da wutar zafin rana tana kawo wa jiki lafiya da kasa baki daya saboda bata gurbata muhalli.
Shi ma Abdu Alhaji Idi wani mai bin digdigin alamuran yau da kullum ya danganta rashin samarda makamashi daga zafin rana da halayen shugabannin da suka shude ne. Yace sun fada tuntuni cewa yayin yin anfani da wutar injina ya wuce. Kamata ya yi a maida hankali wurin yin anfani da rana. Samun makamashi ta zafin rana ya zama rigar zamani, a saki a huta. Saboda haka wajibi ne su yi koyi da takwarorinsu na Morocco wadda ta yi anfani da zafin rana wajen samun makamashinta.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5