NIJAR: An Karrama Wani Masanin Amurka Da Ya Binciko Wadansu Halittun Tarihi

Dr. Paul Sereno

Ofishin jakadancin Amurka a jamhuriyar Nijar ya shirya wani bukin musamman domin karrama Dr Paul Sereno wani dan kasar Amurka dake karantarwa a jami’ar Chicago sakamakon nasarar da aka samu a yayin wani aikin binciken da ya gudanar a gidan ajiyar kayayakin tarihi

i

A watan Disamba da ya gabata ne masani a fannin kayayakin tarihi Dr Paul Sereno malami a jami’ar Chicago da tawagarsa suka je Nijar da nufin tantauna hanyoyin karfafa matakan kariya ga kayayakin tarihin kasar, lamarin da ya basu damar zagaya gidan ajiyar kayan tarihin da ake kira Musse National Boubou Hama, dake Yamai da cibiyar raya al’adu dake garin Agadez aikin da ya samu hadin kan hukumomi da malamai jami’ar Abdulmumuni ta Yamai..

Dr. Paul Sereno ya bayyana Nijar a matsayin kasa dake da dadaden tarihi cike da abubuwan ban mamaki. Masana sun bayyana arewacin Nijar a matsayin wani yankin da bincike ya tabbatar cewa tsohuwar matattara ce ta halittar saboda haka a yayin rangadin na da Dr. Sereno da abokan tafiyarsa ‘yan Nijar da Spaniyawa da kuma Faransawa suka kara zurfafa naziri akan wannan halitta wace yace da zaran ya kale ta ya kan gane wasu sakonni da take dauke da su.

Wata mahawarar da aka shirya a watan yulin da ya gabata a jami’ar Chicago ta karawa wadanan masana kwarin guiwar ci gaba da zurfafa bincike domin kara gano ainihin tushen kayayakin tarihin da Allah ya azurta Nijar da su abinda jakadan Amurka a Nijar Eric P. Whitaker ya yaba da Shi kasancewarsu wata hanyar janyo hankalin ‘yan yawon bude ido.

Saurari cikakken Rahoton Souley Moumouni Barma

Your browser doesn’t support HTML5

An Karrama tarihi Dr Paul Sereno