Nigeria: 'Yan Sanda Na Ci Gaba Da Tsare Dan Jaridar Premium Times

Ibrahim Idris, babban sifeton 'yan sandan Nigeria

Har yanzu 'yan sandan Nigeria na ci gaba da rike Samuel Ogundipe dan jaridan dake aiki da jaridar Premium Times kuma duk da ikirarin da 'yan sandan suka yi cewa maganarsa ta na kotu, babu wanda ya san kotun da suka kaishi ko kuma lokacin da suka kaishi

Har yanzu 'yan sandan Nigeria na ci gaba da tsare dan jaridar Premium Times Samuel Ogundipe wanda suka cafke akan wani rahoton da shugaban 'yan sandan ya rubuta akan mamayar da jami'an DSS suka yiwa majalisun kasar ya kuma mikawa mukaddashin shugaban kasa amma da dan jaridar ya buga a jarida.

Rahoton baban sifeton ya bayyana irin rawar da shugaban hukumar DSS Malam Lawal Daura ya taka abun da kuma ya kaiga tubesh daga mukaminsa.

Ta bakin kakakin babban sifeton 'yan sandan Nigeria Bala Ibrahim abun da dan jaridar ya yi ya sabawa irin horon da ake baiwa 'yan jarida a kasar. Ya na cewa wani abun idan aka fada yana iya tada zaune tsaye ko ma hambare gwamnatin dake ci. Saboda haka ba karamar magana ba ce.

Sai dai duk da ikirarin kakakin babban sifeton, kungiyar Amnesty International ta yi watsi da abubuwan da ya fada. Kakakinta Malam Isa Sanusi ya ce duk maganar ana son a razana 'yan jarida ne domin su tsorata, su gaza yin aikinsu cikin walwala da lumana. Duk maganar da 'yan sandan ke yi shirmen banza ne kawai, injishi.

Ita ma kungiyar 'yan jaridar Nigeria wato, NUJ, ta rubuta wata wasika da kakkausar lafazi zuwa ga mukaddashin shugaban Nigeria ya sa baki domin 'yan sanda su sako dan jaridar Samuel Ogundipe.

Sha'aibu Usman Liman sakataren 'yan jaridar Nigeria ya ce idan za'a je kotu ne a yi shari'a yadda ta dace kungiyarsu ba ta da matsala da hakan. Amma a daina kama 'yan jarida ana musguna masu kafin a kaisu kotu. Ya ce hakan ba daidai ba ne.

Amma kakakin shugaban 'yan sandan Nigeria Bala Ibrahim ya ce su basa rike dashi domin an kaishi kotu. Kotu ce za ta ce ya daina abun da ake tuhumarsa a kai ko kuma ta wankeshi a sakeshi.

Shi ma kamfanin Premium Times ta bakin wani babban jami'inta Malam Sani Tukur ya ce yaushe 'yan sandan suka kaishi kotu, ko sun bi bayan fage ne? Ya ce dokar kasa ta ce duk wanda aka kama ya na da ikon ya nemi lauya saboda haka menene dalilin kaishi a boye?

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina

Your browser doesn’t support HTML5

Nigeria: 'Yan Sanda Na Ci Gaba Da Tsare Dan Jarida Dake Aiki Da Premium Times - 2' 28"