Kisan gilla da wasu miyagun mutane ke yiwa jam’an ‘yan sandan Nigeria yayinda suke bakin aiki na tada hankalin jama’ar kasar.
Makonnin baya ‘yan sanda bakwai ne wasu ‘yan bindiga suka hallaka lokaci guda cikin birnin Abuja. Ba’a dade ba wasu biyu kuma suka rasa ransu duk a cikin Abuja.
A garin Illele dake jihar Rivers wani dan sanda daya ya rasa ransa kana karin wasu uku suka bakunci lahira a jihar ta Rivers. A ranar Lahadi wani dan sanda ya rasa ransa a Bomadi dake jihar Delta. Kazalika ranar aka kashe wasu ‘yan sanda hudu a jihar Kaduna akan hanyarsu ta ceto wadanda ake garkuwa dasu.
Philip Ali Mkana wani dan jihar Edo ne inda wasu ‘yan bindiga suka kasha ‘yan sanda hudu tare da kone motarsu ta sintiri, y ce abun da ya faru bashi da dadi.
Dukka ‘yan sandan an kashesu ne yayinda suke bakin aiki. Wani masanin tsaro Paul Yusuf ya ce akwai sakaci da yawa yanzu cikin jami’an tsaro. Yace sai a sa ‘yan sanda tsaro a wani wuri amma su hudu ko fiye da haka sais u taru kan mota daya suna binciken abun da ba’a san ko menene ba. Idan mutane hudu suna bincike sauran motocin kuma suna wucewa, ba za’a san lokacin da wani mugu zai wuce ba.
Kakakin ‘yan sandan Bala Ibrahim yace lamarin na tada masu hankali dalili ke nan suke zaton akwai siyasa ciki. Ana yi ne domin a katsewa gwamnatin Buhari hanzarin da ta keyi na ganin ta biyawa talaka bukatarsa.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum