Hukumomin Nigeria sun rufe kan iyakokin kasar a dalilin zaben da aka fara yinsa tun daga ran Asabar. Rufe kan iyakokin na Nigeria ya fara aiki ne tun daga karfe goma sha biyun ranar Juma’a har zuwa karfe shida na safiyar lahadi, sannan kuma hukumomin Nigeria suka bada sanarwar daukan matakan rage yawan zairga-zirgar jama’a a lokacin zaben na ‘yan majalisun tarayyar da za’a fara dashi Asabar.
‘Yan Nigeria zasu ziyarci rumfunan zabe domin kada kuri’unsu a zaben da aka kasa shi gida uku a cikin wata guda. Bayan zaben ‘yan majalisar dokokin da za’a gudanar Asabar 2 ga watan Afrilu, sai kuma mako na gaba Asabar 9 ga watan Afrilu a gudanar da na shugaban kasa inda shugaba Goodluck Jonathan ke fuskantar takara tare da tsohon shugaban Gwamnatin mulkin sojin Nigeria, janar Muhammadu Buhari. Zagayen zabe na uku kuma shine na ranar Asabar 16 ga watan Afrilu wanda shine zaben Gwamnonin jihohin Nigeria da na ‘yan majalisar jihohi.