Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi masu sa maye a Nigeria, ta bada sanarwar kama kwayar (Heroin) mai nauyin kilogram dari da talatin da aka yi satar shigar da ita Nigeria daga kasar Iran domin turawa zuwa kasashen turai.
Shugaban hukumar yaki dafatauchin miyagunkwayoyi masu sa maye a Nigeria, Ahmadu Giade, yace an kiyasta kudin hodar Iblis ta (Heroin) da hukumarsa ta kama zasu kai Dala miliyan tara ada dubu dari tara a kasuwa.Ya ce an shigar da hodar Iblis din ne cikin jirgin ruwan ‘yan kasuwa dake dauke da kayan gini. An kama kayan ne a tashar jiragen ruwan birnin Ikko.
Kamen da Nigeria tayi na hodar Iblis ta (Cocaine)daga Iran, yazo ne bayan wata guda da jami’an Nigeria suka kama dilolin dake dauke da muggan makamai daga kasar Iran. Nigeria ta gabatar da kararta gaban kwamatin sulhun MDD saboda karyar dokar kudurin kwamatin sulhun MDD da ya azawa Iran takunkumin saye da saida makamai a kasar waje.