Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Jumma'a Za A Kammala Ayyukan Hajji Na Bana


Yau Jumma'a Za A Kammala Ayyukan Hajji Na Bana
Yau Jumma'a Za A Kammala Ayyukan Hajji Na Bana

Musulmi fiye da miliyan biyu da dubu dari takwas su na shirin kammala ayyukansu na farilla na Hajjin bana a Kasa Mai Tsarki , inda suke yin dawafin ban kwana

Miliyoyin Musulmi alhazai dake Saudi Arabiya a yanzu haka su na gudanar da ayyukan Hajji na karshe kafin su koma kasashensu.

Tuni alhazan da suka kammala aikin jifar shedan, sun kom abirnin Makkatul Mukarrama inda zasu gudanar da Dawafin ban Kwana, watau kewaya Dakin Kaabah sau bakwai da ake yi kafin a kama hanyar komawa gida.

Jiya alhamis, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauka a kan alhazai kimanin miliyan biyu da dubu dari takwas a wurin jifar shedan da kuma a Dakin kaabah inda suek Dawafin na Ban Kwana.

Duk da wannan ruwan sama da aka fara tun daren laraba, an ga dubun dubatan alhazai su na gudanar da ayyukansu na ibada kamar ba ruwan ake yi ba.

Aikin Hajji yana daya daga cikin shika-shikai guda biyar na addinin Musulunci, kuma an wajabta shi ne ga wanda yake da halin zuwa. Wasu Musulmi su kan yi asusu na tsawon rayuwarsu domin su samu zarafin zuwa aikin Hajjin.

A yau Jumma'a za a kammala wannan aiki na Hajji.

XS
SM
MD
LG