A watan Disamban wannan shekara ce gwamnati zata dakatar da shigo da shinkafa ta hanyar ruwa daga ketare, lamarin da ya sa yanzu an samu bullowar kamfanonin sarrafa shinkafa cikin gida.
Duk da wannan ci gaban da aka samu, akwai kalubalen samun abinci cikin farashi mai sauki duk da cewa akwai alamun manoma sun fara cin gajiyar sana'ar ta su.
Jami’an gwamnati a dukan matakai suna cewa gyara nada wuya sai an daure, duk da cewa wasu sun gaji da jin su yi hakuri.
Malam Aminu Bello, kwamishanan kasuwanci na jihar Sokoto, ya ce ba’a iya gina gida rana daya. Ana yi ne sannu a hankali. A cewarsa mulkin da aka canza an yi shekara 16 ana yi har tattalin arziki ya wargaje kafin wannan sabuwar gwamnati ta zo ta shiga gyara gadan gadan. Ya yi kira ga ‘yan Nigeria su ci gaba da yin hakuri da gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari.
Dr. Obadiah Mailafiya, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Nigeria yace, kodashike shugaba Buhari nada muradu masu kyau, yana bukatar kwararru ta fuskar tattalin arziki, matukar ana son a ga cigaba. Ya kamata shugaban ya jawo kwararru domin su taimakeshi saboda ba duka wadanda suke kusa dashi ne suke sonshi ba.
Shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa Hassan Bello, ya ce ‘yan Nigeria sun samu bunkasar fitar da hajjarsu zuwa kasashen waje, kuma da zara an inganta layin dogo a tasoshin kan tudu dake arewacin Nigeria za’a samu bunkasa. Ya ce yanzu ana fitar da abubuwa da yawa saboda manufofin gwamnati.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5