A Najeriya An Kashe Fiyeda Mutane Ashirin A Jerin Hare Hare Da Aka Kai A Jajiberen Kirsimeti.

'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya

Hari mafi munin ya auku ne a Jos,inda ‘Yansanda Asabar din nan suka ce an kashe akalla mutane 20, a wasu fashe fashe har bakwai a wurar biyu.

A jerin hare a hare a jajiberen kirsimeti ranar jumma’a a najeriya,galibinsu a coci coci sun halaka akalla mutane 26.

Hari mafi munin ya auku ne a Jos,inda ‘Yansanda Asabar din nan suka ce an kashe akalla mutane 20, a wasu fashe fashe har bakwai a wurare biyu.

San nan a Maiduguri,hukumomi suka ce ana kyautata zaton ‘yan book Harama sun kai hari da bam da aka hada da mai kan coci uku,suka kashe mutane shida,suka kona wani cocin kurmus.

Cikin wadanda suka mutu harda paston daya daga cikin cocin.

Ana aza galibin hare hare a watannin baya bayan nan kan ‘yansanda da shugabannin yankin kan ‘yan kungiyar.

Gwamnan Jihar Borno,Ali Madu Shariff,yace harin babban abin damuwa ne kuma tilas jami’ai su tabbatar da akwai cikakken tsaro ga masu ibada.