Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Goodluck Jonathan Zai Dauki matakan Yaki Da Ta'addanci


'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya
'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya

A bayan hare-haren bam da aka fuskanta a kasar, shugaban na Najeriya zai nada mai bayarda shawara kan ta'addanci da kuma Kwamitin bin sawun nakiyoyi a kasar

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya zai gabatar da wasu matakan yaki da ta’addanci a kasar, a bayan harin bam da ya kashe mutane 4 ranar jajiberen sabuwar shekara a babban birnin kasar, Abuja.

Kakakin shugaban na Najeriya, Ima Niboro, yace a cikin mako mai zuwa shugaba Jonathan zai nada mai bayar da shawara na musamman kan ta’addanci, da kuma wani Kwamitin shugaba na kula da nakiyoyi a kasar. Har ila yau, kakakin yace za a gudanar da binciken wuraren tara makamai da hukumomin ‘yan sanda suka bada iznin kafawa domin gano inda suke samun makamai, sannan za a kakkafa na’urorin kyamara na sa idanu a duk inda jama’a ke taruwa domin ganin abubuwan dakwe wakana.

Wadannan matakan sun biyo bayan hare-haren bam da tashe-tashen hankulan da aka gani cikin ‘yan watannin nan a Najeriya.

Harin bam na jajiberen sabuwar shekara a Abuja, ya biyo bayan tashin bam a wurin wani gangamin siyasa a kudancin Najeriya da kuma tashin hankalin jajiberen Kirsimeti da ya kashe mutane 80 ya raunata wasu fiye da 100 a garin Jos.

Shugaba Jonathan ya bayyana sabbin hare-haren bam a kasar da suka faro daga harin bam na ranar ‘yanci da ya kashe mutane 12 a Abuja, a zaman wata sabuwa, kuma mummunar barazana, ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar dake shirye-shiryen gudanar da zabe a watan Afrilu.

XS
SM
MD
LG