Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar kwashe ‘yan kasar ta kusan 2000, daga cikin wadanda suka makalle a kasashen ketare sanadiyar annobar cutar coronavirus.
Da ya ke bayani a gaban majalisar dokokin kasar a karshen mako, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar Kalla Hankourao ya bayyana cewa, gwamnati ta kaddamar da ayyukan jigilar ‘yan kasar da suka makalle a kasashen waje sakamakon annobar cutar coronavirus, haka zalika wannan shirin ya ba da damar warware matsalolin al’umomin kasar da matakin rufe iyakokin kasashe ya hana masu dawowa gida.
Ya ci gaba da cewa, zuwa yanzu gwamnatin ta Nijar ta maido ‘yan kasar a kalla 1,817 da suka bukaci a kwashe su zuwa gida, yayin da a daya bangare wasu ‘yan kasar ke nuna alamar har yanzu ba sa ra’ayin a dawo da su.
Tun bayan barkewar annobar coronavirus kungiyar kare hakkin ‘yan cirani ta yi kira ga hukumomin Nijar su dubi halin da ‘yan kasar ke ciki a ketare da idon rahama, a saboda haka shugaban kungiyar JIMED Manou Nabara Hamidou ya yaba da wannan yunkuri na gwamnati.
Gwamnatin ta Nijar ta jaddada aniyar ci gaba da maido da ‘yan kasar da matakin rufe iyakokin kasashen waje ya tilastawa zama sanadiyar annobar COVID-19 da ta addabi duniya a yanzu haka.
Har ila yau gwamnatin Nijar ta fara sassauta da dama daga cikin matakan da ta shimfida bayan barkewar cutar coronavirus.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5