Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla Biyu Sun Mutu A Yakin Libiya Jiya Asabar


Janar Khalifa Haftar na LNA
Janar Khalifa Haftar na LNA

Mutane akalla biyu sun riga mu gidan gaskiya a wani barin wuta da aka yi jiya Asabar a mafakar mutanen da su ka rasa muhallansu, a cewar Hukumar Kai Daukin Gaggawa wadda ke wani sashe na Tripoli babban birnin kasar Libiya, wanda ya yi ta shan barin wuta daga mayakan gabashin kasar da ke kokarin maida babban birnin kasar a karkashin ikonsu.

Wannan luguden wuta ya haddasa gobara a mafakar wadda ke gundumar Fornaj, wadda ke daura da wani fagen daga da kuma matsugunin mutanen da suka rasa muhallansu a fadace-fadacenn da su ka gabata, a cewar Usman Ali, mai magana da yawun hukumar kai daukin gaggawa da kuma samar da motocin ambulas.

Ali ya ce hukumar ta kai daukin gaggawa na kokarin ta kwashe sauran mutanen da ke cikin mafakar ta kai su wani wurin a cikin birnin. Dama mutanen da ke zaune a mafakar ta Fornaj akasari sun fito ne daga gundumar Ain Zara da ke kusa da wurin.

Fighters of a military battalion loyal to Libyan General Khalifa Hafta patrol the streets in the eastern city of Benghazi during a state of emergency to combat the coronavirus disease outbreak, March 21, 2020.
Fighters of a military battalion loyal to Libyan General Khalifa Hafta patrol the streets in the eastern city of Benghazi during a state of emergency to combat the coronavirus disease outbreak, March 21, 2020.

(Wasu dakarun da ke biyayya ga Janar Haftar kenan ke sintiri a wani titi na birnin Benghazi da ke gabashin kasar)

Mayakan, wadanda ke kiran kansu Sojojin Kasa Na Libiya (LNA a takaice), sun kaddamar da wani hari watanni 13 da su ka gabata a yinkurinsu na kwato Tripoli, inda fadar gwamnatin Hadin Kan Kasa (GNA, a takaice) ta ke, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da halarcinta.

A watan jiya Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi hudu cikin biyar na fararen hulan da su ka samu lahani a yakin basasar Libiya a cikin watanni uku na farkon shekarar 2020, sojojin LNA ne su ka ji masu, sojojin da ke samun goyon bayan daga Hadaddiyar Daular Larabawa, da Masar da kuma Rasha.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG