Tun a ranar 5 ga watan nan na fabreru ne ya kamata kowane daga cikin ‘yan takarar 2 ya sanarda hukumar sadarwa matsayinsa game da wannan mahawara sai dai Izuwa ranar litinin 8 ga wata dan takarar RDR Canji Mahaman Ousman bai waiwayi hukumar ta CSC ba a yayinda ana sa gefe abokin fafatawarsa Bazoum Mohamed ya karbi goron gayyata mafari kenan aka sauke mahawarar in ji shugaban hukumar CSC Dr Kabirou Sani.
Jigo a jam’iyar PNDS Tarayya Adamou Manzo dake alfahari da gogewar dan takararsu akan maganar shugabanci na cewa rashin abin fada ne ya hana Mahaman Ousman yin na’am da gayyatar da hukumar CSC a wannan mahawara.
To sai dai kakakin jam’iyar RDR Canji Alhaji Doudou Rahama na alakanta abin da wasu dalilai masu nasaba da ajandar yakin zaben da Mahaman Ousman ke gudanarwa a jihohi.
Dokokin ayyukan sadarwa da sha’anin gudanar da zaben Nijer sun tanadi tsarin shirya mahawara a tsakanin ‘yan takarar da suka yi nasarar zuwa zagaye na 2 na zaben shugaban kasa domin baiwa ‘yan kasa damar cashe aya da tsakuwa to sai dai cika wannan ka’ida ya faskara domin ko a shekarar 2016 ma mahawarar da ya kamata a yi a tsakanin Issouhou Mahamadou da Hama Amadou ba ta yiwu ba saboda a wancan lokaci jagoran na ‘yan hamayya Hama Amadou na tsare a gidan yarin Filingue sanadiyar hukuncin da aka yi masa a game da zargin safarar jarirai.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5