Karawar karshe an yi ta ne tsakanin Kadiri Abdou da aka fi sani da Issaka Issaka dan kokowar jihar Dosso da kuma Sabo Abdoulaye dan kokowar birnin Yamai, inda Issaka Issaka ya samu nasarar lashe takobin kwambalar, kamar yadda Aboukar Isa wakilin Muryar Amurka ya bada rahoto.
An kwashe kusan minti 15 ana fafatawa tsakanin Kadiri Abdou da Sabo Abdoulaye, kafin Issaka Issaka ya samu galaba a kan Sabo Abdoulaye.
Wannan shi ne karo na biyar da dan kokowar na Dosso Issaka Issaka ke lashe takobi a kwambalar kokowar gargajiya, a karon farko a shekarar 2015 a jihar Agadez, da shekarar 2016 a jihar Dosso, da shekarar 2019 a jihar Tilabery, da shekarar 2021 a birnin Yamai, sai kuma a baya bayan nan a Jihar Diffa.
A yanzu dai ana iya cewa, Issaka Issaka shi ne dan kokawar gargajiyar Nijar da ya fi yawon kai takobi a jiharsa a tarihin kokowar gargajiyar Nijar, wanda ya samu shiga gaban Kantu na Maradi mai takobi hudu.
Kamar kowace shekara, manyan baki daga Najeriya sun je kallon kwambalar ta kokowar gargajiya a bana.
Duk da matsalar tsaron da jihar Diffa ke fuskanta an yaba matuka da yadda jihar ta shirya wannan gasar karo na 43.
Kwanaki dai goma aka kwashe ana fafatawa tsakanin ‘yan kokowar gargajiyar Nijar 80 da suka fito daga jihohi takwas na kasar. A shekarar 1975 aka soma kokowar gargajiyar domin sada zumunta tsakanin dukkan jihohin Nijar.