Birnin Nkonni, Niger —
Zamu soma labarun wassanin mu na ranar yau da jamhuriyar Nijer,inda yan wassan kwallon kafar kasar yan kasa da shekaru 17 suka kasa kan labari a wassanin yanki na 2 na wafo ko UFOA na neman shiga kopin nahiyar Africa na kwallon kafa na wannan ajin da ke wakana a babban Birnin Yamai yanzu haka.
Kasar ta Nijer, ta kasa yin katabus ne a wannan kombalar, bayan da yan wassan ta suka sha kashi a karawar su ta farko a hannun Cote d'Ivoire ko Ivary Coast, kamin tayi kunnan doki da kasashen Benin da Togo.
A kasar Britaniya kuwa, a jiya ne kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta hadu da cikas a kokarin ta na karkarewa a matsayin ta 4 a teburin kakar bana ta Firimiya Ligue ta kasar Ingila, bayan da ta sha kashi 0 - 2 a hannun Newcastle.
A yau Saouthampton na karbar bakuncin Liverpool.
Arsenal yanzu haka tana matsayin ta 5 maki 66, bayan Tottenam dake da maki 68, yayin da a ke cigaba da yin kankankan tsakanin Liverpool da Man - City a saman teburin Firimiya Ligue ta Ingila.
Idan Liverpool tayi nasara a yau din nan, zata kasance maki guda ne ke da tseraya tsakanin ta Man City kamin wasannin karshen Firimiya ligue na wannan shekara a karshen wannan makon.
A wasann
in serie A na kasar Italiya, a ranar jiya ne Juventus ta karfafa matsayin ta na 4 a teburin serie A bayan tayi 2 - 2 da kungiyar kwallon kafa ta Lazio de Rome a Turin.
A karshen wannan wasar, Paulo Dybala da Giorgio Chiellini sunyi ban kwana da magoya bayan kungiyar ta Juventus.
Giorgio Chiellini ya buga wa Juventus wasanni har so 560 yayin da Paulo Dybala ya buga wasanni 292 wa club din Juventus.
Saurari rahoton Harouna Mammane Bako:
Your browser doesn’t support HTML5