An tuhumi wani mutum guda da laifin harin da aka kai a wasu masallatai biyu a kasar New Zealand wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 49.
Harin ya kuma jikkata wasu mutum 48.
Shugaban ‘yan sanda, Mike Bush ya ce za a gurfanar da mutumin a gaban kotu a gobe Asabar.
Ko da yake, Bush bai ambaci sunan mutumin da ake tuhuma ba, amma gidan talbijin din kasar na TVNZ ya bayyana wani dan bindiga mai suna Brenton Tarrant daga Grafton na yankin South Wales na kasar Australia a matsayin wanda ya kai harin.
Hukumomin kasar Australia sun tabbatar da cewa mutumin dan kasarsu ne.
Har ila yau, an kama wasu mutum hudu – maza uku mace guda. Firai minitar kasar New Zealand Jacinda Ardern, ta ce babu ko daya daga cikin mutanen da ake sa mai ido.
Daga cikin wadanda suka jikkata suke kan karbar magani har da kananan yara a cikinsu.
Akalla mutum 41 da aka kashe a masallaci guda ne.