A yau Litinin, Isra’ila ta fara bikin tunawa da cika shekara guda da zagayowar ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da kungiyar Hamas ta kaddamar da mummunan hari akanta, inda ake nuna alhini a wuraren da aka yi kisan kiyashi tare da gudanar da tarurrukan dake neman a dawo da wadanda aka yi garkuwa dasu gida.
An shirya gudanar da shagulgula a fadin Isra’ila da manyan biranen duniya domin tunawa da zagayowar ranar da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawan dake zirin Gaza ta kaddamar da harin, daya hallaka fiye da mutane 1, 200.
Shugaba Isaac Herzog ya kaddamar da bukukuwan ta hanyar yin shiru na wani dan lokaci da misalin karfe 6 da mintuna 29 na safe-sa’ilin da aka kaddamar da harin-a garin Kibbutz Reeim, wurin da ake tsaka da gudanar da bikin raye-raye da wake-wake sa’ilin da mayakan Hamas suka hallaka akalla mutane 370 a mummunan harin nan na ranar 7 ga watan Oktoba.
Iyalin wadanda aka hallaka sun halarci bikin tunawa da zagayowar ranar, galibinsu suna cikin kuka, lokacin da Shugaba Herzog ke ganawa da malarta taron, kamar yadda wakilin kafar yada labarai afp ta ruwaito.
Shi kuma Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya lashi takobin dawo da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su "A wannan rana kuma a wannan wuri da kuma wurare da dama a kasarmu muna tunawa da waɗanda aka kashe da kuma waɗanda aka yi garkuwa da su."
Tun bayan wannan rana da aka kai hare-haren, Falasɗinawa kusan 42,000 aka kashe a zirin Gaza a cewa ma'aikatar lafiyar Hamas
A jiya Lahadi, dubun dubatar al’umma sun halarci irin wadannan bukukuwa a fadin duniya, domin jajantawa wadanda harin Hamas ya shafa tare da bayyana goyon baya ga al’ummar Falasdinawa bayan shafe shekara guda suna fuskantar yaki a zirin Gaza.