Netanyahu na Israila da Putin Na Rasha Sun Gana

Firayim Ministan Israila Natanyahu da Shugaban Rasha Putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun yarda da tsara daukar matakan soja a tsakanin kasashensu a ciki da wajen Syria don kare barazanar karawar bazata

Sun hadu ne a jiya Litinin a gidan Shugaban kasar Rasha da ke Novo-Ogar’vovo da ke wajen birnin Mascow.

Netanyahu ya fadawa manema labarai cewa, “Ni da Putin mun yarda da tsara abinda zai kare duk wata sabanin fahimta a Tsakaninmu.”

Ya kuma tabbatar da cewa, tattaunawar tasu ta wakana cikin yanayin girmamawa da mutunta juna.

Taron dai na ranar Litinin din ya biyo bayan rahotannin da ke cewa Rasha na kera jirgin yakin soja da kuma ajiye sojoji a Syria don taimakawa Bashar Al-Assad.

Rasha tana taimakawa gwamnatin Syria ne wajen yakin da ta keyi da ‘yan tawayen da suke neman hambarar da gwamnatin.