Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Israila Ya Kira Taron Gaggawa


Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu
Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu

Biyo bayan yaduwar rikici tsakanin Yahudawa da Falasdinawa a birnin Qudus Firayim Ministan Israila ya kira taron tattaunawa cikin gaggawa

Jiya Litinin Frayim Ministan Israila ya kira taron gaggawa da ministocinsa domin su tattauna cikin gaggawa yaduwar tashin hankali tsakanin Yahudawa da Falasdinawa a birnin Qudus.

Da safiyar jiya wani bayahude ya rasa ransa yayinda motarsa ta fada cikin wani rami sakamakon rokar Falasdinawa da ta fada kan motar. Wasu mutane biyu dake cikin motar su ma sun ji rauni.

Kazalika jiyan ma Falasdinawa da suka fara zanga zanga tun ranar Lahadi sun kara da 'yansanda a gabashin Qudus kusa da wurin ibada dake da mahimmanci ga Yahudawa da Musulmai.

Musulmai na kiran wurin masallacin al-Aqsa yayinda Yahudawa na kiransa Tudun Ibada.

A karkashin wata yarjejeniya da aka cimma tun da dadewa Yahudawa ke kula da harabar masallacin to amma Musulmai ne kadai aka amincewa su yi salla a masallacin.

Cikin wasikar da ya rubutawa Hukumar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya jakadan Falasdinawa Riyad Mansour ya zargi jami'an tsaron Israila da hana Larabawa yin ibada a masallacin. Saboda haka ya bukaci hukumar da ta tashi ta yi aikinta da jan kunnen Israila ta daina tsokana.

To amma ita Israila ta zargi Falasdinawan da yin anfani da karfin soji domin su hana Yahudawa zuwa harabar masallacin yayinda suke bikin sabuwar shekararsu.

A birnin Washington DC fadar gwamnatin Amurka mai magana da yawun ma'aikatar harkokin kasar John Kirby yace Amurka ta yi tur da kakkausan lafazi tashin hankalin dake faruwa a birnin Qudus tsakanin bangarorin biyu. Yace wajiibi ne bangarorin su kai zuciya nesa su bar tsokana da kalamu ko wasu take take na takala.

XS
SM
MD
LG