Neman Aiki Ya Zama Aiki Mata Ku Tashi Tsaye

Aisha Saleh

An bukaci mata dasu jajirce wajen neman ilimi sannan su nemi sana’ar hannu musammam ma ga matasa ‘yan mata da ma zawarawa domin su zamo masu tsayawa a kan kafafunsu,

Aisha Saleh, wata matashiyar bazawara ce ta bayyanawa DandalinVOA hakan a yayin zantawarta da Baraka Bashir, inda ta ke cewa don auren mace bai yi karko ba bai kamata zuciyarta ta mace ba.

Ta kara da cewa da zarar wata kofa ta rufe wata budewa ta ke, inda ta ce bayan aurenta bai yi nasara ba sai ta koma makaranta tun daga tushe inda ta sake jarabbawar WAEC ta nemi gurbin karatu a jami’a i ta kuma sami takardar Diploma, kammalawarta ke da yuwa sai ta sake neman gurbin karatun degree.

Daga bisani sai ta canza ra'ayi ta koma kasar Ghana inda ta karanci aikin jarida , a hannu guda kuma tana gudanar da sana’arta domin kashe kananan bukatu.

Aisha ta ce gama karantunta ke da yuwa sai neman aiki ya zama aiki, ko da yake a lokacin da take kararunta a kasar Ghana ta ce ta fuskanci matsalolin musammam ganin yanayin karatunsu da na Nijeriya akwai bambanci matuka inda a kasar Ghana komai a komfuta ake yinsa .

Your browser doesn’t support HTML5

Neman Aiki Ya Zama Aiki - 6'02"