Hukumar bada agajin ,gaggawa ta NEMA a Najeriya tare da sauran wasu cibiyoyin agaji na duniya sun hada hannun yadda zasu koyawa 'yan gudun hijira a yankunansu na Najeriya sana'o'in hannu don dogaro da kai.
WASHINGTON DC —
Talauci da wahalhalun rayuwa na daya daga abubuwan da ke dama lissafin ‘yan gudun hijirar da ke arewa maso gabashin Najeriya sakamakon rikicin boko haram.
Musamman a yayin da wasu matan suka rasa mazajensu da ke tallafawa rayuwarsu da ta ‘ya’yansu. Wannan ce tasa aka fito da shirin koyar da sana’o’in hannu ga ‘yan gudun hijarar.
Domin su sami damar ci gaba da tallafar kansu da ta ‘ya’yan da ke gabansu. Ta yaya za’a yi wannan lamari har ya kankama? Abokin aikinmu Mahmud Lalo ya hada mana wannan rahoton na musamman, tare da taimakon wakilinmu Ibrahim Abdulaziz daga jihar Adamawa.
Ana iya sauraron cikakken rahoton a makalar sautin da ke kasa.
Your browser doesn’t support HTML5