NEMA: Ta Ilimantar da Mutane Akan Ambaliyar Ruwa

Ambaliyar Ruwa

Kowace shakara akan samu ambaliyar ruwa da kan yi sanadiyar asarar dukiyoyi masu dimbin yawa, saboda haka hukumar bada agajin gaggawa ko NEMA ta soma taron ilimantar da jama'a.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya ko NEMA ta shiga ilimantar da jama'a akan yadda zasu kaucewa amabaliyar ruwa da ake fama dashi kowace damina.

Saboda haka hukumar tayi wani taron wayar da kawunan jama'a a jihar Neja akan yadda zasu kare kansu lokacin damina. A baya an sha fama da ambaliyar ruwa da ke jawo asarar dukiya da ma rayuka muddin idan ruwan sama ya zo da garfi da guguwa.

Hukumar harsashen yanayi a Najerita tayi harsashen cewa daminanr bana ba zata zo da wuri ba. Akwai kuma yiwuwar daminar ba zata dauki dogon lokaci ba amma ana iya yin ruwan sama da karfi.

Mr Lugard Misalaku babban jami'in NEMA a jihohin arewa ta tsakiya yace lokacin da za'a yi ruwa watakila ya zo da yawa. Idan ba'a shirya ba kuma ya zo da yawa za'a samu matsala. Dalili ke nan suke gayawa mutane su kiyaye da abubuwan da aka gaya masu na fadakarwa. Misali idan mutun manomi ne to ya san cewa bana ruwan sama ba zai dade ba kamar yadda aka saba.

Wani kalubale da hukumar NEMA ke fuskanta ita ce yadda wani lokaci mutane ke yin watsi da shawarwarin da aka basu. Sai matsala ta taso su rasa na yi.

Ga karin bayanin Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

NEMA: Ta Ilimantar da Mutane Akan Ambaliyar Ruwa