WASHINGTON, DC —
Hukumar yaki da fataucin muyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta cafke wani gawurtatcen dililalin kwayoyi, mai suna shayo Oguntegbe, wanda akafi sani da Oritano.
Jami’in hukumar a jahar ta Ekiti, Mr. Nnanna Nworisa, ne ya bayana wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, a Ado Ekiti.
Mr. Nworisa, yace jami’an hukumar ta NDLEA, sun cafke shi ne a wani samame da suka kai a daya daga cikin manyan gonakinsa inda yake noma tabar We-We, a garin Ikere-Ekiti, bayan da jami’an suka kwashe kwanaki 21, suna biye da shi tsakanin jahohin Ondo, Osun da Ekiti.
Hukumar tace ta kama mutane talatin da biyu inda biyun suka kasance mata ne a watan Agustan da ta gabata da tabar We-We mai nauyin kilo gram kusan 280.