Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yar-Tsana Da Tafi Kowace Jaririya Tsada A Duniya


Yar tsanar jaririya
Yar tsanar jaririya

Jiya da rana tsaka wasu mutane suka kira jami’an ‘yan sanda na garin Oaklan a jihar California, cikin gaggawa. Inda suka ga wata jaririya cikin mota, kuma babu kowa a tare da ita. Wannan dai ya razana mutane da dama, isar jami’an ‘yan sanda ke da wuya, sai suka yi kokarin fasa gilashin motar, domin ceto rayuwar wanna jaririyar.

A tabakin dan sanda Mr. Johnna Watson, mudai a karon farko, tunanin mu ya zamuyi mu ceto rayuwar wanna yarinyar, kamin ma mu fara maganar motar waye, kuma me yasa suka bar jaririya a cikin mota da rana tsaka, babu kowa a tare da ita.

Gama fasa gilashin motar ke da wuya, sai suka ga cewar ashe wanna ba jaririyar gaske bace, ashe jaririyar wasan yara ce. Bayan sun fahimci cewar wanna ba jaririyar gaske ba ce, sai suke bada wata sanarwa cewar, duk inda mutane suka ga irin haka, to su hanzarta sanar da hukumomi don gaggauta isa wajen don bada taimakon gaggawa.

Anyi kira da jama’a da su guji irin wanna dabi’ar, domin irin wanna kan iya haifar da wata matsala da ba’asan mai zata haifar ba a gaba. Kuma suna kokarin suga wanna mai motan domin jin dalilin yin wanna abun.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG