Bisa ga gayyatar Shugaban Amurka Donald Trump,Shugaban Najeriya Muhammad Buhari zai fara ziyarar aiki a nan Amurka daga ranar 29 ga wannan watan.
Ana kyautata zato a ganawar shugabannin biyu zasu tattauna alamuran tsaro da cinikayya da dai wasu abubuwa makamantansu, musamman matakan da ita Amurka zata dauka wajen taimakawa Najeriya da yaki da ta’addanci da kuma cin hanci da rashawa.
Dr. Usman Muhammad wani mai sharhi akan alamuran diflomasiya da sha’anin kasa da kasa ya yi tsokaci akan abubuwan da yake gani zasu yi tasiri a wannan ganawar ta shugabannin.
A ganin Dr Usman akwai batun yaki da shugaba Buhari ya keyi da cin hanci da rashawa. Ya ce akwai kudade da yawa da Amurka ta kwace daga wasu da suka hada da tsohuwar minister man fetur wadda take da kudade da gidaje a wasu jihohin Amurka. Za’a yi maganar ta da wasu barayin da suka boye kudade a kasar Amurka.
Baicin hakan akwai bayanan sirri da Shugaba Buhari bai sani ba da za’a shaida masa.
Abu na biyu shi ne maganar yaki da Boko Haram da yawan tashin hankali dake aukuwa a wurare daban daban cikin kasar, musamman kashe-kashen da a keyi a jihar Binuwai tsakanin makiyaya da manoma. Amurka zata bayyana irin taimakon da zata ba Najeriya.
Dr Usman yace gwamnatin Amurka na iya ba Shugaba Buhari bayanai akan wasu mukarrabansa da suke da hannu dumu-dumu cikin cin hanci da rashawa a Najeriya.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5