Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yayi amai ya lashe. Ya canza matsayinsa gameda kafa kasar Falasdinu. Yanzu yace ba zai taba goyon bayan a kafa kasar Falasdinu ba idan har aka sake zabensa a zaben kasar da ake yi yau Talata.
Mr. Netanyahu yayi magana kwana daya kamin zaben kasar, inda masu zabe miliyan shida 'yan kasar zasu tafi rumfunan zabe domin yanke shawara ko shugaban jam'iyyar masu ra'ayin rikau din zai sami wa'adi na hudu a zaman Firayim Ministan kasar.
Kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a na baya bayan nan ta nuna Mr Netanyahu yana bayan jam'iyyar Zionist hadakar jam'iyu karkashin jagorancin wani dan siyasar kasar da ake kira Isaac Herzog.
Ganin babu daya daga cikin 'yan takarar da ake jin zai sami rinjaye a majalisar dokokin kasar mai kujeru 61, 'yan takara sun zafafa yakin neman goyon bayan kananan jam'iyu da suka hada da ta 'yan komunist, da kuma ta larabawa da kuma ta mabiya addinin yahudu sau da kafa.