Da yake jawabi a wurin wani taron manyan malaman addinin Kirista da na Musulmi a jihar Kaduna, gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i ya ce gwamnatinsa zata bi-biyi tashe tashen hankulan da aka samu har guda Goma sha Biyar, da kuma tabbatar da hukunta duk wadanda aka samu da hannu a ciki.
Wasu daga cikin manyan malaman addinan da suka halarci wannan taro sun jingina matsalar tsaron a kan rashin gudanar da irin wannan taro na manyan malaman addinan da zasu taimaka wajan samar da zaman lafiya da tsaro a jihar Kaduna.
Sai dai kuma limamin masallacin juma’a na Al-Munnar, Sheik Tukur Al’munnar, ya zo da mabanbancin ra’ayi, inda ya bayyana cewa duk maganar zaman lafiyar da za’a yi bata kai wadda ke cikin littattafan addinan biyu ba, dan haka a nasa ra’ayi, malaman addinan ne ya kamata su gayyaci gwamnati domin bata shawara a maimakon ita ta gayyace su.
Malamin ya kara da cewa idan aka wayi gari malaman addinan biyu suka bada tabbacin zaman lafiya a jihar Kaduna, babu shakka haka zata cimma ruwa domin alhakin ya rataya ne a kawunansu.
Wannan shine karo na farko da gwamnatin El-Rufa’i, cikin kusan shekaru biyu ta tattara manyan malaman addinin Kirista da na musulmi domin tattaunawa akan matsalolin tsaro da suka addabi jihar.
Isa Lawal Ikara, ya aiko mana da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5